• Labaran yau

  NSCDC ta gurfanar da matashi gaban kotu bisa zargin aikata luwadi a Argungu

  Daga Isyaku Garba |

  Hukumar NSCDC ta jihar Kebbi,ranar Juma'a, ta gurfanar da wani matashi mai suna Bashar Samaila gaban wata Kotun Majestare a garin Birnin Kebbi bisa zargin aikata luwadi.

  Mai gabatar da kara Ast.Insp Habibu Sani ya shaida wa Kotu cewa "Wani lokaci a cikin watan Satumba Bashar Samaila mazauni garin Kangiwa ya keta mutuncin wani yaro mai suna Abubakar Muh'd ta hanyar taushe shi ya aikata luwadi a cikin garin Argungu".

  Habibu Sani ya kara da cewa bayan wanda ake tuhumar ya aikata luwadin ya kuma shafa wa yaron Chemical .Mai gabatar da kara ya ce wannan ya saba wa sashe na 284 da 245 dokokin Penal Code na jihar Kebbi  .

  Mai shari'a Majestare Atiku Abubakar ya tambayi wanda ake tuhuma ko ya aminta da tuhumar da ake masa shi kuma wanda ake tuhuma ya musanta lamarin. Sakamakon haka Majestare Atiku Abubakar ya umarci mai gabatar da kara su hanzarta kammala bincike kan lamarin .

  Kotu ta dage sauraron karar har zuwa ranar 20 ga watan Satumba domin ci gaba da shari'ar ta kuma tasa keyar wanda ake zargin zuwa gidan Kurkuku kafin ta sami shawara daga ofishin mai gabatar da kara na Gwamnati DPP.

  Sakataren kungiyar Mata 'yan Jarida na Arewa maso yamma Khadiza Sa'idu tare da hadin Gwuiwar Kungiyar Lauyoyi Mata na Najeriya ce ke jagorantar tabbatar da adalci a wanni lamari mai ban tausayi ganin cewa wanda aka cutar talakawa ne.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: NSCDC ta gurfanar da matashi gaban kotu bisa zargin aikata luwadi a Argungu Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama