• Labaran yau

  November 05, 2017

  Barawo ya makale a windo bayan yayi yunkurin shiga gida domin ya yi sata (Hotuna)

  'Yansanda a West Midlands na kasar Ingila sun ceto wani barawo da ya makale a windon wani gida yayin da ya yi yunkurin shiga gidan domin ya yi sata.

  Saurayin da 'yansandan suka kama ya makale ne gangan jikinsa na cikin gidan yayin da kafafuwansa suna waje.

  'Yansandan sun ce saurayin ya kasance a wannan yanayi har tsawon awa biyar lamarin da ya sa ya yi ta ihu domin neman taimako.

  Wani dattijo da ya fara ganinsa yaki ya taimaka masa ganin yanayin da saurayin ya ke ciki,amma ya kira 'yansanda daga  West Midlands wanda suka zo suka kubutar da shi kuma suka saka masa ankwa suka tafi da shi ofishinsu.  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Barawo ya makale a windo bayan yayi yunkurin shiga gida domin ya yi sata (Hotuna) Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama