• Labaran yau

  Bayanai daga komputar Osama sun nuna yana sha'awar kallon wakokin India da Tom & Jerry

  Isyaku Garba |

  Wasu sabin bayanai da CIA ta fitar wadda ke bayanin irin fina-finai da sauran ababe da aka samu a cikin Komputar shugaban kungiyar Alqaida Osama Bin Ladin sun nuna cewa Bin Ladin yana sha'awar kallon wasan Tom & Jerry a wasu bayanai da hukumar ta CIA ta tattaro daga Komputar marigayin tun 2 ga watan Mayu na 2011 bayan zaratan sojoji na musamman na kasar Amurka sun kashe shi a wani tsararren shirin farmaki na sirri da suka kai a maboyarsa a Abbottabad na kasar Pakistan.

  Yawan bayanai da hukumar CIA ta samu a Komputar Bin Ladin sun kai 321 GB wadda ya kunshi sauti,bidiyo, fail-fail kusan 4,70,000.

  Mutumin da ya taba kasancewa lamba daya daga cikin jerin mutanen da hukumar bincike ta FBI ke nema a Duniya ya kasance mai sha'awar kallon fina-finan yara na Tom & Jerry, Antz, Chicken Little da Cars.

  Haka zalika Bin Ladin yana kallon wasar "Best FIFA World Cup Goals".Akwai kuma wakokin fina-finan India da yake kallo a Komputarsa kamar wakokin ‘Ajnabee mujhko itna bata’ daga fim na Pyar Toh Hona Hi Tha, da Dil Tera Aashiq har da  ‘Tu chand hai poonam ka’ daga fim da aka yi a 1994  Jaane Tamanna.

  Bayan wadannan akwai wasu shairye -shirye wadda aka nada dauke da bayanin tarihin shi kansa Osama Bin Ladin wadda BBC ta yi da kuma wasu faya-fayin bidiyo na National Geographic Videos wadanda suka kunshi World's Worst Venom, Inside the Green Berets, da kuma Kung Fu Killers.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Bayanai daga komputar Osama sun nuna yana sha'awar kallon wakokin India da Tom & Jerry Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama