An fara shari'ar 'yan kungiyar boko haram fiye da 5000

An fara shari'ar 'yan kungiyar boko haram wadanda ke tsare a hannun sojin Najeriya a wani yanayi na sirri da aka samar da Alkalai hudu da zasu yi wa fiye da mutum 5000 'yan kungiyar ta boko haram shari'a.

BBC ta labarta cewa za'a fara shara'ar 'ya'yan kungiyar ne a Kainji inda ake tsare da fiye da 'yan boko haram fiye da 16000 a wani wajen da aka tanada domin tsare 'yan kungiyar.

Fiye da mutum 1,670 ne za'a yi masu shari'a a 'yan makonni masu zuwa daga bisani kuma a fuskanci sauran daya bayan daya.

Wannan shine shari'a kan harkar ta'addanci mafi girma da za'a gudanar a tarihin Najeriya.Wasu daga cikin wadanda aka kama sun shafe kusan shekara 4 a tsare bisa tanadin dokokin ta'addanci.

Ministan shari'a Abubakar Malami yace za'a dauki watanni ana shari'ar ta la'akari da yawan wadanda ake zargin.

Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
An fara shari'ar 'yan kungiyar boko haram fiye da 5000 An fara shari'ar 'yan kungiyar boko haram fiye da 5000 Reviewed by on October 10, 2017 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

ISYAKU TV

Powered by Blogger.