Tsohon babban kwamandan dakarun sojin kasa na Najeriya Victor Malu ya mutu

Tsohon babban hafsa kuma kwamandan dakarun kasa na sojin Najeriya karkashin gwamnatin shugaba Olusegun Obasanjo Lt.Gen. Victor Malu ya mutu da sanyin safiyar Litinin a wani Asibiti a Cairo babban birnin kasar Masar watau Egypt.

Malu ya mutu yana da shekar 70.Ya rike mukamin babban kwamandan dakarun sojin kiyaye zaman lafiya na kasashen yammacin Afirka watau ECOMOG daga watan Agusta 1996 zuwa Janairu 1998 kuma babban kwamandan dakarun kasa ta Najeriya daga watan Mayu 1999 zuwa watan Afrilu na 2001.

Lt.Gen Malu shine shugaban kotun soji da ta saurari shari'ar tsohon mataimakin shugaba Janar Sani Abacha Gen.Oladipo Diya,da Gen Olaronwaju,Gen Adisa da sauran hafsoshin soji bayan an zarge su da hannu a yunkurin juyin mulki a zamanin Janar Abacha a 1998.

Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN