• Labaran yau

  China ta ci wani Hotel tara domin ya ba Musulmi masauki

  Hukumomi a yankin kudancin Guangdong na kasar Sin watau China sun ci taran wani Hotel a wani gari da ke yankin kan iyaka na Shenzhen saboda ya ba wasu Musulmi 'yan Uyghur masauki.

  Rahotanni sun nuna cewa 'yan sanda a kasar ta China sun haramta saukar da baki daga yankin Xinjiang na gabacin kasar saboda galibinsu Musulmi ne.

  Wani ma'aikaci a daya daga cikin Hotel da ke yankin Shenzhen ya shaida wa gidan Radiyon Free Asia cewa 'yansanda sun ci Hotel da yake aiki taran  15,000 yuan kimanin dalan Amurka $2,260 saboda karya dokar da aka gindaya.

  Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: China ta ci wani Hotel tara domin ya ba Musulmi masauki Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama