• Labaran yau

  June 07, 2017

  Najeriya ta biya masu fallasa kudin sata Naira miliyan 375 | isyaku.com

  Gwamnatin Najeriya ta ware Naira miliyan 375.8 don biyan masu fallasa kudaden sata 20 da suka taimaka hukumomin kasar wajan gano Naira Biliyan 11.6.


  A cikin wata sanarwa da ta fitar, Ma’aikatar Kudin kasar da ta tabbatar da sakin kudaden ta ce, a karon farko kenan da ake biyan mutane karkashin tsarin fallasa kudaden satar.

  Sai dai gwamnati ba ta bada bayani ba game da mutanen da suka amfana da kudaden saboda dalilai na tsaro.

  Ma’aikatar Kudin ta ce, matakin biyan ya nuna irin yadda gwamnatin Muhammadu Buhari ta mayar da hankali don cika alkawarinta ga masu fallasar, wadda ke da muhimmanci wajen yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya.

  Gwamnati na bai wa masu fallasar akalla kashi 5 cikin 100 na kudaden da suka bayar da bayanansu kuma aka gano su, amma an tanadi hukuncin dauri a gidan yari kan duk wanda ya fallasa bayanan karya.
  @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka aiko mana rahotu ? ka tuntube mu a birninkebbi080@gmail.com


  Daga RFI
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Najeriya ta biya masu fallasa kudin sata Naira miliyan 375 | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama