El-rufai ya umarci a kama Matasa masu kishin Arewa | isyaku.com

Gwamna Nasir El-rufai na jihar Kaduna ya umarci kwamishinan 'yansanda na jihar ya kama duk wadanda suka sa hannu a abin da aka kira da "ayyanawa na Kaduna" inda aka ba 'yan kabilar ibo mazauna Arewacin Najeriya wata uku su fice daga Arewacin Najeriya su koma kudu.

Haka zalika Gwamnan ya umarci babban mai shara'a da kwamishinan shara'a na jihar Kaduna su shirya tuhuma akan wadanda ake zargi a bisa hurumin "ingiza jama'a".

A jiya ne wasu Matasa masu kishin Arewa suka sanar a wani taro cewa 'yan asalin kabilar ibo mazauna Arewa su koma kudu yayin da 'yan Arewa mazauna kudu suma su dawo Arewa a cikin wata uku.

A yayin da yake jawabi wa taron manema labarai mai magana da yawun kungiyar Abdulazeez Suleiman yace "kabilar ibo sun dade suna wulakanta 'yan Najeriya musamman 'yan Arewa ta hanyar cin zarafin hadaka da amanar Najeriya a matsayin kasa daya,raina sauran 'yan Najeriya da nuna kasaita da girman kai ga sauran 'yan Najeriya da sauransu.

Ya kuma kara da cewa "Daga yau 6 ga watan Yuni 2017,da akasa sanya hannu a wannan ayyanawa,kasar Arewa mai muhimmanci a harkokin Najeriya ba zata sake amincewa da ibo ba kuma zata yi duk abinda ya dace ta tabbatar ta kawo karshen hadaka da kabilar ibo a Najeriya"

Suleiman ya ci gaba da cewa "Dukuyoyi da kadarorin ibo zasu kasance na kasar arewa kuma zasu nada kwamiti da zai fara tantance dukiyar ibo da ke zaune a Arewa kafin a fara gudanar da tsarin".

Akalla kungiyoyi tara na matasan Arewa ne suka sa hannu a wannan takardar "ayyanawa" wanda suka hada da Arewa Citizens Action for Change,Arewa Youths Consultative Forum,Arewa Students Forum da sauran su.


Arewa Citizens Action for Change, Arewa Youths Consultative Forum, Arewa Youths Development Foundation, Area Students Forum, and northern Emancipation Network. Others are Northern Youths vanguard, Northern Youths Stakeholders Forum, North East Assembly and North Central Peoples Front.

Read more at: http://www.vanguardngr.com/2017/06/breaking-el-rufai-orders-arrest-northern-youths/

@isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka aiko mana rahotu ? ka tuntube mu a birninkebbi080@gmail.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN