• Labaran yau

  June 26, 2017

  Mutum 153 sun kone kurmus da ransu | isyaku.com

  Kimanin mutum 153 ne suka kama da wuta kuma suka kone kurmus a yayin da wata motar tanka da ta dauko man fetur ta fadi kuma ta jirkice kana tayi bindiga daga karshe ta kama da wuta a birnin Bahawalpur da ke gundumar Punjab na kasar Pakistan.

  Bayanai sun nuna cewa wadanda hatsarin ya rutsa da su mutane ne da suka je wajen da man fetur ya malala saboda su debi man fetur din wanda tsautsayi ya rutsa da su motar ta kama da wuta a yayin da suke dibar fetur .

  Gabadayan yankin ya kidime sakamakon aukuwar wannan lamarin da tuni masu bayar da agajin gaggawa suke ta bayar da gudunmawa ga wadanda suka jikata sakamakon shakar gurbataccen iskar da konewar motar ya haifar.

  Bayanai sun nuna cewa an sami cinkoson jama'a da suka je su debi man fetur din ne sakamakon karancin man fetur din a wannan yankin wanda rinjayen wadanda suka rasa rayukkansu a wajen 'yan kewayen birnin ne Bahawalpur ne.


  Ku biyo mu a shafin mu na Facebook @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari. Kana da sha'awar taimaka mana da Labarai, ko sharhi ? ka kira mu a 08062543120
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Mutum 153 sun kone kurmus da ransu | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama