Birnin kebbi: Bikin karamar Sallah | isyaku.com

Da misalin karfe 8:30 na safiyar yau Lahadi 25/6/2017 Limamin babban Masallacin jihar Kebbi Alh.Muhktar (Walin Gwandu) ya jagoranci Sallar Idi a harabar Masallacin Idi wanda ke cikin harabar Sakatariyar Haliru Abdu a cikin garin birnin Kebbi.

An tashi cikin ni'ima yau a garin Birnin Kebbi yayin da giragizar suka lullube garin wanda hakan ya haifar da saukar yayyafin ruwan sama amma takaitacce.

Imam Muhktar yayi nasiha wadatacce inda ya tanatar da Musulmi akan su zabura su tsaya a bisa kafafuwan su wajen dogara da kawunan su,ya kuma yi nasiha akan muhimmancin hadinkai a cikin al'umma Musulmi da dai sauran nasihohi da suka wadata.

Wani abin sha'awa shine binciken mu ya nuna mana cewa a karamar Sallar bana ba'a sami rarraba na ranar Sallah ba.A garin Birnin kebbi kusan ko ina a cikin birni da kewaye Musulmi sun ajiye Azumi  kuma suka Sallaci karamar Sallah a yau Lahadi.Sabanin yadda akayi ta fama da banbancin ranakun Sallah a can baya a tsakanin Al'umma.

Wakilinmun ya shaida mana cewa titunan garin Birnin kebbi sun fuskanci karancin ababen hawa musamman da rana,wanda hakan bai rasa nasaba da hutawa da jama'a ke yi ba sakamakon samun hutun Sallah.

A kowane unguwar kamar yadda aka saba a kasar Hausa lokacin bukukuwan Sallah,yara kanana da Mata ne ke zagayawa inda suke sada zumunci tsakanin 'yan uwa da abokan arziki.


Ku biyo mu a shafin mu na Facebook @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari. Kana da sha'awar taimaka mana da Labarai, ko sharhi ? ka kira mu a 08062543120.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN