'Muryar Buhari ta ba ni tsoro' - inji wani dan Najeriya | isyaku.com

Wasu masu sharhi a Najeriya suna fargabar cewa rashin lafiyar Shugaban Kasar Muhammadu Buhari ta tabarbare bayan da ya aike da sakon saukin muryarsa.

Shugaban ya aike da saƙon bikin ƙaramar sallah ne ga 'yan Najeriya ranar Asabar.
Lokacin ne karon farko da aka ji duriyarsa bayan ya kwashe kwana 49 yana jinya a Birtaniya.

Hakan ya sa jama'a sun rika bayyana ra'ayoyinsu a kafofin sada zumunta a kasar, inda wasu suke cewa "muryarsa tana nuna cewa rashin lafiyarsa ya yi tsanani."

Yayin da wasu ke cewa muryarsa ba ta sauya ba daga yadda suka santa ranar da zai tafi jinya Landan.

Malam Kabiru Danladi Lawanti na Fannin Koyar da Aikin Jarida na Jami'ar Ahamdu Bello ta Zariya, ya ce halin rashin lafiyar "shugaban ya yi tsanani."

"Duk wanda ya san Shugaba Buhari kuma ya saurari muryar da aka sanya ranar Asabar to wajibi ne ya tsorata."
"Za ka ji muryar tana shakewa kamar wanda ya kamu da mura." in ji Lawanti.

Ya ci gaba da cewa: "Idan ka saurari muryar da kyau za ka ji babu kuzarin da aka saba ji idan yana magana."

Ko lokaci ya yi da Buhari zai jefar da kwallon mangoro?

Har ila yau, malamin jami'ar ya yi tsokaci game da kiraye-kirayen da wasu ke yi na cewa lokaci ya yi da shugaban zai yi murabus.

"Batun murabus abu ne mai tsarkakiya. Abu ne na doka da kuma siyasa, amma idan ya kasance shugaban baya iya tafiyar da mulki, to abu mafi alheri a gareshi shi ne ya yi murabus," in ji shi.

Ya kara da cewa: "Yanzu ka ga ya yi kwana 40 yana jinya. Ni a nawa ra'ayin idan da zai yi wata uku a cikin wannan hali - babu abin da ya sauya. To ni ma ina da ra'ayin gara kawai ya yi murabus. Don lafiyarsa ta fi komai."Ku biyo mu a shafin mu na Faceboo @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari. Kana da sha'awar taimaka mana da Labarai, ko sharhi ? ka kira mu a 08062543120.DOWNLOAD OUR APPLICATION.APK

Daga BBC

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN