Zaharaddeen:DSS ta amince kafin na shirya fim da ya nuna labarin Boko Haram


Zaharaddeen Sani sanannen jarumin nan a Kannywood ya ce ya sami amincewar Hukumar 'yan sandan Asiri ta DSS da kuma hukumar tantance finafinai na Kasa kafin ya yi fin dinsa na ABU HASSAN wanda ke nuna rikicin Boko Haram.

Zaharadden ya shaida wa jaridar Premium Times a yayin da yake hira da ita cewa,ya fuskanci wasu matsaloli da farko,wanda ya danganci tsaro ta hanyar yadda aka yi amfani da kakin Soja da bindigogi da abubuwan da suka shafi tarzoma.

A cikin fin din mai suna ABU HASSAN wanda shi ne na farko da aka taba yin iransa a Kannywood an nuna yadda wata kungiya mai da'awar ta'addanci ta addabi jama'a amma daga bisani an nuna yadda Sojoji suka ci galabar kungiyar a karshen shirin.

@isyakuweb--Ku biyo mu a shafin mu na Facebook
https://web.facebook.com/isyakuweb


Zaharaddeen:DSS ta amince kafin na shirya fim da ya nuna labarin Boko Haram Zaharaddeen:DSS ta amince kafin na shirya fim da ya nuna labarin Boko Haram Reviewed by on March 24, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.