• Labaran yau

  Birnin kebbi: Ofishin JAMB,bama fifita wasu wajen rijista

  Akwai zarge zargen cewa Ofishin kula da harkokin jarabawa na shiga jami'oin Najeriya (JAMB) da ke garin Birnin kebbi tana fifita 'yayan wasu manyan Mutane a wajen shigar da sunayen yaran a na'urar kwamputa domin yin rajista sabanin bin layi kamar yadda sauran yaran wadanda basu da galihu ke yi.

  ISYAKU.COM yayi tattaki zuwa wannan ofishin inda muka gani da ido yadda aka dauki matakan tsaro musamman daga kofar shiga ofishin inda ake tantance yaro ko yarinya kafin a bari a shiga.Duk da yake akwai yara masu son su yi wannan rijistan wanda hakan ya haifar da kwarya kwaryar cikonso a bakin ofishin,amma jami'an ofishin sun dukufa domin sun gudanar da aikin kamar yadda ya kamata.

  A yayin da yake maida jawabi game da lamarin mukaddashin shugaban ofishin na JAMB a Birnin kebbi ya ce wannan zarge zargen suna fitowa ne daga mutane da basa son gaskiya wanda aka shirya domin a karkatar da sahihancin lamari,ya kara da cewa zargine da baya da tushe kuma wadanda ke cewa haka mutane ne da suka bukaci jami'an ofishin su aikata rashin gaskiya amma hakar su bata cin ma ruwa ba shi yasa suke wannan korafe korafen da babu tushe.

  Shugaban hukummar ya ce a bana kawai a jihar Kebbi an sami fiye da yara 7000 da sukayi rajista da JAMB domin neman shiga jami'oin Najerya.


  @isyakuweb--ku biyo mu a Facebook
  https://web.facebook.com/isyakuweb
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Birnin kebbi: Ofishin JAMB,bama fifita wasu wajen rijista Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });