An kama 'yan Boko Haram a Ekiti





Hukumomin tsaro sun ce sun kama wani dan kungiyar Boko Haram a jihar Ekiti.


A wata sanarwa da babban jami’in hukumar tsaro ta farin kaya DSS Tony Opuiyo ya fitar, ya ce jami’an su sun kai farmaki a sassa daban-daban na Nijeriya, inda su ka kama ‘yan ta’adda da masu son tada zaune tsaye da dama.

Ya kara da cewa, a ranar Litinin da ta gabata ne, hadin gwiwar rundujar soji da ta DSS ta kama mutumin da ake zargin dan Boko Haram ne mai suna Adenoyi Abdulsalam a birnin Ado Ekiti.

A cewar sa, kafin a kama Abdulsalam, an kai farmaki a kan mayakan Boko Haram da dama a arewacin Nijeriya, wadanda su ka hada da jihohin Bauchi, da Yobe, da Gombe, da Nasarawa, da Kaduna da kuma Kogi.

Opuiyo ya kara da cewa, a cikin wadanda aka kama har da wani dan Boko Haram mai suna Usman Ladan Rawa, wanda ake yi wa lakabi da Mr X a Lafia ta jihar Nasarawa.

Haka kuma, an kama wani dan Boko Haram mai suna Nasiru Sani, wanda ake yi wa lakabi da Osama a Bauchi, yayin da aka kama wani dan Boko Haram mai suna Adamu Jibrin.



(Liberty)@isyakuweb--Ku biyo mu a Facebook
https://web.facebook.com/isyakuweb

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN