• Labaran yau

  March 05, 2017

  Birnin kebbi, wani mutum ya banka wuta a wani gida


  An sami tashin gobara a unguwar Makerar Gago da ke cikin garin Birnin kebbi da rana a gidan wani bawan Allah mai suna Nura wanda aka tabbatar da cewa wani ne ya sa wutar amma kuma ba wanda ya san dalilin da ya sa aka sa wutar ,lokacin da Matar Nura ta ga mutum ya fito daga gidan su,kuma
  sai wuta ta tashi daga wani daki wanda aka ajiye ciyawar abincin dabbobi wanda ake kyautata zaton cewa wanda ya fito daga gidan ne ya haddasa.Wutar ta yi sanadin zama gobara da ta kama wani bangare na gidan.

  Ganin hakan ne ya sa Matar Nura ta ruga waje tana neman taimako,ganin haka sai wani matashi ya ruga domin ya taimaka,sai wanda ya sa wutar ya fitar da wukake guda biyu,bayan haka kuma wasu mutane sun sake yin yunkuri domin su damke wanda ya sanya wutar, nan kuma ya sake fiddo wukake guda biyu sanadin haka ya sa ba'a kama shi ba,kuma ba'a gane ko waye ba.

  Abin mamaki shi ne idan irin wannan abin zai dinga faruwa a cikin tsakiyar gari a cikin mutane kuma da tsakiyar rana kikiri,lallai abin ya  zama abin tsoro a wannan lokaci da muke ciki.A bisa wannan dalili ne muke kira ga hukumomin da abin ya shafa su dauki mataki akan wannan al'amari,da kuma kara inganta tsaro a cikin al'umma.

  SHARHI 

  Idan za ku tuna irin wadannan abubuwa na aikata manyan laifukka na faruwa a cikin garin Birnin kebbi,amma har ila yau hukumomi basu gano masu aikata wadannan aika-aika ba.Misali a nan shi ne matsalar wani bawan Allah da ake zargin an kashe a bara a Rafin Atiku ta hanyar yankawa,na biyu kuma sai zancen Matar da aka daddatsa ta bayan an kashe wasu yara guda hudu a tare da ita a unguwar Bayan kara a bara,sai kuma 'yan Achaba da akayi ta kashewa wanda har yanzu dubun masu aikata wannan aikin bai cika ba a hukumance.

  Isyaku Garba
  @isyakuweb  Ku biyo mu a Facebook
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Birnin kebbi, wani mutum ya banka wuta a wani gida Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama