• Labaran yau

  Kebbi,Majalisar dokoki ta dakatar da 'Yan majalisa 2 har tsawon wata 6

  Majalisar Dokoki ta jihar Kebbi ta dakatar da wasu 'Yan Majalisa su biyu har tsawon wata shida, saboda aikata ba daidai ba,dakatarwar ya na nufin ba za'a yi wata harka da ta shafi ayyukan Majalisa ba tare da su har tsawon adadin wannan lokacin.


  A bayanin da ya yi wa manema labarai jiya a Birnin kebbi,shugaban kwamitin ladabtarwa na Majalisar dokoki ta jihar Kebbi Hon.Barista Hamza ND Bello yace sun dauki matakin ne saboda rahotanni na tsaro da suka samu cewar 'yan Majalisar su biyu suna cikin Mutanen da suka dinga yi wa Mai girma Gwamnan jihar Kebbi ihu lokacin da ake zanga-zanga yayin da Gwamna Atiku Bagudu ya kai ziyarar ta'aziyya a garin Suru a ranar Litinin.

  Majiyar mu ta kara da cewa Jagoran 'yan Majalisar Hon.Yakubu Bello,shi ne wanda ya gabatar da kudurin a gaban majalisa kuma 'yan majalisa da gaggarumin rinjaye suka dauki matakin dakatar da 'yan Majalisar su biyu.Bayanai sun nuna cewa,za a bukaci wadanda abin ya shafa da cewa su rubuta takardar neman afuwa zuwa ga Gwamna da 'yan Majalisa bayan wa'adin dakatarwar su ta kare.

  Isyaku Garba
  @isyakuweb  Ku biyo mu a Facebook


  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kebbi,Majalisar dokoki ta dakatar da 'Yan majalisa 2 har tsawon wata 6 Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });