Yi Amfani Da Man Kwakwa Wajen Gyara Kwalliya


Man kwakwa yana da matukar amfani kuma yana cikin jerin kayan abinci da za mu iya kira da abinci mai nagarta, yana da sinadarai masu samar wa da dan adam koshin lafiya da kuzari wanda suka hada da rage kiba, karfin kwakwalwa, karfin aiki da dai wasu ababe masu yawan gaske.
Ga kadan daga cikin ayyukansa
1. Taushin fata – Ana iya shafawa kamar man jiki a shafa ko’ina har wuya.
2. Man fuska – Ana shafawa a zagaye kwayar ido da shi yana maganin bakin da ke fitowa zagaye ido, yana maganin tamushewar fata na tsufa, kuma ana iya shafa man kwakwa a jikin auduga a goge fuska dashi, yana maganin cire kwalliya da ta dankare a fuskar mata
3. Kwantar da fata yayin aski – Man kwakwa yana gyarawa masu aski, kamar maza masu yawan yin kurajen fuska da na keya sakamakon aski, gyaran fuska da sauransu, yana warkar da kurajen
4. Man goge hakora – akwai magungunan wanke baki da dama amma wannan na daban ne, ana hada man kwakwa da ‘baking soda’ a gauraya dan kadan a sa a ‘burushi’ a goge baki da shi
5. Man kwakwa yana gyara jikin jarirai musamman ma irin masu yin ciwon Ella, wanda shi ciwon nan har cikin gashin su ya ke shiga, To uwa ta dage da gogawa yaro man kwakwa insha Allahu zai warke
6. Yana gyara gashin mata, yana sa gashi ya yi kyau, ya yi laushi yana kyali, ya kuma kashe wani amosani ko kwarkwata da ke kan mace
7. Yana maganin cututukan fata da dama kamar su kyasbi, kunan wuta, kunar rana, da cututuka da dama. Kuma ana iya hada man kwakwa da suga a murza a fata, sannan a wanke da ruwa da sabulu yana sa fata ta yi lukwi-lukwi
8. Yana hana fashewar lebe, musamman a lokacin sanyi.

MUJALLARMU

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN