Ba za'a karbi kudin aikin Hajji na bai daya ba a Hajjin bana

Hukumar kula da jin dadin Alhazai ta Najeriya ta ce ba za'a karbi kudin aikin HajjH na bai daya ba daga maniyyata aikin Hajji na 2017.Shugaban huka na kasa NAHCON Abdullahi Mohammad ya shaida wa manema labarai a Abuja ranar Laraba.Ya kara da cewa Hukumar ta yi haka ne domin ta sauwaka wa maniyyata aikin Hajji ta la'akari da halin da ake ciki na tattalin arzikin Najeriya.

Shugaban hukumar ya ce adadin kudin aikin Hajjin bana zai banbanta daga jiha zuwa jiha ta yin la'akari da irin tsarin da jihohi zasu yi ma maniyyatan jihohin nasu.Ya kuma ce yin haka zai sa Mahajjata su sami ingantaccen kulawa daga hukumomin alhazai na jihohin su.

@isyakuweb-- Shafin mu a Facebook
https://web.facebook.com/isyakuwebBa za'a karbi kudin aikin Hajji na bai daya ba a Hajjin bana Ba za'a karbi kudin aikin Hajji na bai daya ba a Hajjin bana Reviewed by on March 23, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.