Majalisa Ta Bukaci a Tsige Hameed Ali

Majalisar Dattawan Nijeriya ta bukaci shugaba Muhammadu Buhari da ya tsige shugaban hukumar kwastam Hameed Ali daga kujerar sa.

Wannan na zuwa ne bayan da Hameed Ali ya ki gabatar da kansa a gaban majalisar a yau Laraba.
Majalisar ta ce, Hameed Ali bai cancaci ya rike wani mukamin shugabanci ba.
Rikici tsakanin Hameed Ali da majalisar ta fara ne bayan da hukumar ta sanar da wani shirin ta na karbar kudaden haraji akan tsoffin motocin da aka riga aka shigo da su kasar.
Majalisar ta gayyaci Hameed Ali domin ya zo ya yi bayani akan wannan shiri, ta kuma bukaci ya sanya khakin kwastam idan zai zo.

Hameed Ali ya je majalisar bayan gayyata ta biyu, amma ba da khaki ba, al’amarin da ya sanya majalisar ta ki sauraran sa a ranar, ta ce masa ya je ya dawo sati mai zuwa sanye da khaki.
Kafin satin ya zagayo ne majalisar ta samu wasika daga ofishin ministan shari’a na kasa, Abubakar Malami da ke sanar da ita cewa Hameed ba zai kara gabatar da kansa a gabanta ba saboda wani ya shigar da kara akan batun sanya khakin.

A yanzu haka dai majalisar a karkashin shugabancin Sanata Bukola Saraki ta yi watsi da wasikar Malami.

(Mujallarmu)
@isyakuweb - Shafin mu na Facebook
https://web.facebook.com/isyakuweb


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN