Jami'ar ABU tace Dino Malaye ya kammala karatunsa na Digiri

Rahotanni sun tabbatar da cewa shugaban Jami'ar Ahmadu Bello ABU da ke Zaria na jihar Kaduna Ibrahim Garba ya tabbatar da cewa Sanata Dino Malaye ya kammala karatunsa a Jami'ar ta ABU.Shugaban ya baiyana haka ne a yau Litinin a yayin da yake amsa tambayoyi a gaban taron Kwamitin bincike da Majalisa ta kafa.

A makon da ya gabata ne Jaridar Sahara Reporters ta wallafa wani rahoto da ke zargin sanatan da yin amfani da takardun jabu saboda bai kammala karatunsa na digiri ba.

Ibrahim Garba ya shaida wa kwamitin cewa Jami'ar ta shaida sunan Dino wanda suka sani a Daniel Jonah Malaye cewa ya kammala karatunsa na Digiri a ajin sakamako na 3 "watau 3rd class"

@isyakuweb--Shafin mu na Facebook
https://web.facebook.com/isyakuweb

Jami'ar ABU tace Dino Malaye ya kammala karatunsa na Digiri Jami'ar ABU tace Dino Malaye ya kammala karatunsa na Digiri Reviewed by on March 28, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.