• Labaran yau

  Ejent Babawo ya ziyarci jihar Kebbi domin zakulo kwararru a kwallon kafa

  A yau dinnan wani Ejent mai zawarcin 'yan wasan kwallon kafa mai suna Babawo Muhammed Adamu ya ziyarci garin Birnin Kebbi babban birnin jihar Kebbi domin ya zakulo shahararrun 'yan wasan kwallo da ake da su a jihar Kebbi domin shirin gabatar dasu a mataki na gaba wanda hakan zai zama shimfida ta samun daukaka ta kulawa daga manyan kungiyoyin kawallon kafa ta Naajeriya har izuwa kasashen Turai.

  Babawo ya shaida wa ISYAKU.COM cewa wannan shine karo na farko da ya ziyarci jihar ta Kebbi,ya kuma nuna gamsuwarshi a kan yadda ya ga 'yan wasa suna taka leda ta hanyar salon buga kwallo wanda ya gani da idon sa a babban filin wasa ta Gwamnati ta Haliru Abdu,wanda a haka ne ya gamsu da salon wani dan wasa da ake kira Sa'adu kuma yayi alkawarin cewa zasu nazarci yiwuwar daukar dan wasan zuwa mataki na gaba.

  Babawo ya ce suna zagayawa fadin Najeriya ne domin su zakulo 'yan kwallo masu hazaka domin su tsara masu shiri na matakin samun ingantaccen kulawa ta hanyar sadasu da manyan Kulob-Kulob na kwallon kafa a Najeriya da kasashen Turai .Ya ce izuwa yanzu,ya sami kimani yan wasa 60 daga wasu bangarori na Najeriya shi yasa yanzu ya mayar da akalarsa zuwa Arewacin Najeriya,ya kara da cewa daga nan zai zarce ne zuwa Sokoto.

  Kalli bidiyo a kasa
  @isyakuweb--Shafin mu na Facebook
  https://web.facebook.com/isyakuweb


  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Ejent Babawo ya ziyarci jihar Kebbi domin zakulo kwararru a kwallon kafa Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });