Matashin Da Ya Gillewa Tsohuwa Mai Shekaru 72 Kai

Rundunar ‘yan sanda jahar Ogun ta kama wannan matashi dan shekaru 23 a bisa zargin guntilewa wata tsohuwa ‘yar shekara 72 kai.Wannan al’amari dai ya faru ne a yankin Abigi da ke jahar.Mai magana da yawun ‘yan sandan jahar Abimbola Oyeyemi ya tabbatar da faruwar al’amarin. Ya ce sun kama matashin mai suna Adeoye Ikugbayigbe ne bayan da dan matar mai suna Ekundayo Shada ya kawo masu kara.

Shada ya fadawa ‘yan sanda cewa a ranar 17 ga watan Maris, ya na kan hanyar sa zuwa gona inda zai je ganin babar sa ne ya hadu da Adeoye dauke da jakar leda. Da ganin sa, sai Adeoye ya ajiye ledar ya zuba da gudu, al’amarin da ya bashi mamaki.Bayan ya isa gonar ne ya ce ya nemi babar sa ya rasa, sai ya dawo ga bakar ledar. Ya ce ya shiga dimuwa da ya ga kan babar sa ne a cikin ledar.Da ya kai rahoton wajen ‘yan sanda, sun zuba jami’an su a jejin da ke keyawe da yankin, inda daga bisani suka kama Adeoye.

A fadar ‘yan sandan, Adeoye ya amsa laifin sa, ya kuma ce ya aikata hakan ne saboda rikicin da suke matar akan wata gona.Tuni dai aka ajiye gawar matar, tare da kan a dakin ajiyar gawarwaki. Haka zalika ‘yan sanda sun samo addar da matashin ya yi amfani da ita wajen aikata laifin.


Alummata

@isyakuweb--Shafin mu na Facebook
https://web.facebook.com/isyakuweb

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN