Trump ya yi watsi da hukuncin kotu

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi watsi da hukuncin da wata kotun kasar ta yanke, da ta dakatar da umarnin da ya bada na haramtawa wasu ...


Shugaban Amurka Donald Trump ya yi watsi da hukuncin da wata kotun kasar ta yanke, da ta dakatar da umarnin da ya bada na haramtawa wasu 'yan kasashe 7 da musulmai suka yawa shiga kasar.
Mista Trump ya yi ta wallafa wasu bayanai a shafinsa na tweeter, inda ya ke cewa, hukuncin da alkalin kotun ya yanke, ba zai yi wani tasiri ba kuma shirme ne kawai.
Ya kuma kara da cewa akwai hadarin gaske, matukar za a bari mutane su yi ta kwarara Amurka.
Amurkawa da dama ne dai suka fito tituna dan nuna adawa da matakin Mista Trump tare da yin kalaman batanci a gare shi.
Ana saran Amurkawa za su sake yin wata zanga-zangar a birnin Washington, da Miamai da sauransu.
A bangare guda kuma yawancin kamfanin jiragen sama sun ci gaba da dauko fasinjojin kasashen da aka hana din.
Tun lokacin da yake yakin neman zabe, Mista Trump ya yi alkawarin zai kawo karshen kwararowar baki 'yan cirani kasar.
Da alkawarin gina katanga tsakanin Amurka da Mexico, duk dai a kokarin takaita shigowar 'yan cirani da 'yan gudun hijira kasar.
Da alwashin haramtawa musulmai shiga Amurka, wanda hakan ya fusata wasu 'yan kasar da suke ganin ya yi wa kundin tsarin mulki karan tsaye.
Wanda bai amince a fifita wani addini kan wani ba, ko mai da wani addini saniyar ware.
BBCHausa

COMMENTS

Name

AL-AJABI,25,BIDIYO,1,BIRNIN-KEBBI,26,DUNIYA,23,FADAKARWA,23,FASAHA,3,HOTUNA,41,JAKAR MAGORI,20,LABARI,426,NISHADI,51,SANARWA,13,SHARHI,13,SIYASA,17,TARIHI,7,WASANNI,8,
ltr
item
ISYAKU.COM: Trump ya yi watsi da hukuncin kotu
Trump ya yi watsi da hukuncin kotu
https://3.bp.blogspot.com/-jbkOrnRtiGc/WJbXe21oI5I/AAAAAAAACkc/HwpwBiYv9gcPalmvv2xzhAanM2ydUoEwgCEw/s320/_93966665_4d7a74d8-f92c-494e-aa46-5338a306d930.jpg
https://3.bp.blogspot.com/-jbkOrnRtiGc/WJbXe21oI5I/AAAAAAAACkc/HwpwBiYv9gcPalmvv2xzhAanM2ydUoEwgCEw/s72-c/_93966665_4d7a74d8-f92c-494e-aa46-5338a306d930.jpg
ISYAKU.COM
http://www.isyaku.com/2017/02/trump-ya-yi-watsi-da-hukuncin-kotu.html
http://www.isyaku.com/
http://www.isyaku.com/
http://www.isyaku.com/2017/02/trump-ya-yi-watsi-da-hukuncin-kotu.html
true
3052478943858316060
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts KARANTA SAURAN LABARAI Karanta saura Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All KARANTA WADANNAN LABEL MAADANI BINCIKA GABADAYAN LABARAI Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS CONTENT IS PREMIUM Please share to unlock Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy