HATSARI YA RUTSA DA WANI DAN ACABA A TITIN BADARIYA - BIRNIN KEBBI

Wani hadari ya faru a kan titin Badariya a cikin garin Birnin kebbi ,wannan lamarin ya faru ne a yayin da wani karamin yaro ya ketaro kan titin ba tare da kulawa ba,shi kuma dan acaban bai dau hankalin cewa yaron zai ketara ba hakan ya haifar da yunkurin kauce wa yaron da dan acaban yayi sai ya fadi da babur din sa.
Ya sami raunukka a fuskar shi da sauran bangarorin jikin shi,amma bayan suma na takaitaccen lokaci,bawan Allah ya mike kan kafafun shi,kuma wasu abokan shi sun taimaka suka dauke shi zuwa Assibiti.

HATSARI YA RUTSA DA WANI DAN ACABA A TITIN BADARIYA - BIRNIN KEBBI HATSARI YA RUTSA DA WANI DAN ACABA A TITIN BADARIYA - BIRNIN KEBBI Reviewed by on January 18, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.