Yan sanda a jihar Legas sun cafke wasu ‘yan fashi da makami guda biyu da suka kware wajen fesa barkono domin yin fashi wa masu tuka babura.
Wadanda ake zargin dai sun kai hari kan wani direban babur ne a kokarinsu na kwace masa babur din a lokacin da mazauna unguwar gadar Obasanjo da ke Alagbado suka kama su, suka mika su ga ‘yan sanda.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Ben Hundeyin, wanda ya tabbatar da kamun ya ce ‘yan sandan na bin sauran ‘yan kungiyar.
“A ranar 15/02/24 da misalin karfe 07:30 na safe, an samu rahoton wani direban babur cewa da misalin karfe 06:30 na safe wasu mutane biyu wadanda aka bayyana sunayensu da Ayuba Oyegbele da Ojo Gbolahan suka tare shi a Ogo Oluwa, Alagbado. ya kai su gadar Obasanjo,” in ji PPRO.
“Amma da isa ga gadar Obasanjo, Ojo Gbolahan ya sauko ya yi kamar yana son ya biya mai babur ne.
“Amma a maimakon haka sai ya fito da busasshiyar barkono ya hura a idon mai babur kuma ana cikin haka ne sai biyun suka fara dukan mai babur da nufin su yi masa fashin babur.
“An yi sa’a, masu wucewa da suka ga yadda mai babur ke ihun neman agaji, sun zagaya don ceto shi, yayin da wadanda ake zargin suka yi yunkurin tserewa.
“An fi karfinsu aka cafke su aka kai su ofishin ‘yan sanda na Alagbado.
“Bincike ya nuna cewa wadanda ake zargin sun saba yi wa masu babura fashi,” ya kara da cewa.
From ISYAKU.COM