Kwanaki 5 da hukuncin Kotun Koli, Sarakuna sun ki taya Abba murnar galaba kan APC


Legit Hausa ya wallafa cewa kwanaki biyar kenan da kotun koli ta tabbatar da Mai girma Abba Kabir Yusuf a matsayin zababben gwamnan jihar Kano.

Har zuwa safiyar Laraba da ake tattara rahoton nan, Sarakunan jihar Kano ba su fito sun taya gwamna Abba Kabir Yusuf murna ba.

Hukuncin ya kawo karshen doguwar shari’ar zabe da gwamnan ya yi da APC wanda ta tsaida Nasiru Yusuf Gawuna a takarar 2023.

A cikin wadanda suka aika da sakon farin ciki zuwa ga gwamnan har da jagororin PDP kamar Atiku Abubakar da Bukola Saraki.

Sarakunan da ake da su wadanda gwamnatin Dr. Abdullahi Umar Ganduje ta kirkira, ba suyi wani jawabi kamar yadda aka sa rai ba.

A matsayinsu na iyayen kasa, ba a ji sun taya gwamna murna ko kira ga APC da ‘dan takaranta, Nasiru Gawuna su dauki kaddara ba.

Salisu Hotoro wanda yake taimakawa Abba Kabir Yusuf a kafafen zamani ya yi ikirarin Masarautar Misau ta taya mai gidansa murna.

Kamar yadda ya fitar da takarda a Facebook, Hotoro ya ce Sarkin Misau, Alhaji Ahmad Sulaiman ya taya Abba murnar galaba kotu.

A ranar Litinin, gwamna Abba Kabir Yusuf ya hadu da Mai martaba Aminu Ado Bayero wajen bikin tunawa da mazan jiya da aka yi.

Legit Hausa ba ta da masaniya a kan wainar da aka toya tsakanin Sarki da gwamna Abba sai dai wasu sun fara kiran canza Mai martaba.

Sarakunan su ne na Kano, Rano, Karaye, Gaya, da Bichi wanda ake zargin an kawo domin su kishiyanci Malam Muhammadu Sanusi II.

A karshe gwamnatin APC ta cirewa Muhammadu Sanusi II, ta nada Aminu Ado Bayero, yanzu wasu suna kawo shawarar dawo da shi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN