Wani jami’in sojan Najeriya ya kashe kansa a wani barikin sojoji da ke Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.
Sojan mai suna Boyi Thanksgod, yana tare da runduna ta 35 Artillery Brigade, Alamala a Abeokuta. Rahotanni sun bayyana cewa, ya harbe kansa ne a lokacin da suke bakin aiki a ranar tunawa da sojojin kasar.
Ana ci gaba da gudanar da bincike don gano abin da ya haddasa lamarin wanda ya faru a ranar Litinin, 15 ga watan Janairu.
From ISYAKU.COM