Kano: An Sake Bijiro da Sabon Al'amari Kan Kujerar Sunusi Lamido Bayan Nasarar Abba Kabir


Tun bayan nasarar Gwamna Abba Kabir a Kotun Koli, aka fara kiraye-kirayen dawo da tsohon Sarkin Kano, Sunusi Lamido Sunusi.

Magoya bayan gwamnan sun bukaci a sake duba dokar da ta tabbatar da masarautun jihar don dawo da Sunusi Lamido kan kujerarshi. Legit Hausa ya wallafa.

Idan ba a mantaba, tsohon gwamnan jihar, Abdulllahi Ganduje shi ya tube Sunusi a kujerar Sarkin Kano a shekarar 2020.

Sai dai magoya bayan gwamnan yayin da suka fito tarbar Abba Kabir a Kano sun yi ta shelar cewa "Sabon Gwamna, sabon Sarki", cewar Leadership.

Wannan kira har ila yau, ta karade kafofin sadarwa don ganin an dawo da tsohon sarkin, kamar yadda Daily Trust ta tattaro.

A ranar 29 ga watan Mayu bayan Abba Kabir ya karbi rantsuwa ya yi magana kan matakin dawo da Sunusi Lamido Sunusi kan kujerar.

Abba ya ce bai yanke wani hukunci ko wata shawara ba game da masarautun da tsohon gwamnan jihar ya kirkiro.

Martanin na shi na zuwa ne bayan jita-jitar cewa da zarar ya hau karagar mulki zai rusa sabbin masarautun a jihar.

Wata majiya ta tabbatar da cewa lamarin na kara girma wanda ake tunanin yin Sola don turawa Majalisar jihar kan sabunta dokar masarautun.


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN