Daga hana shi shan tabar wiwi a kusa da Masallaci saurayi ya caka wa Liman wuka har lahira a Kano


Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta cafke wani kasurgumin dan daba mai suna Yusuf Haruna AKA Lagwatsani mai shekaru 18 bisa laifin kashe wani fitaccen limami mai suna Malam Sani Mohammed Shuaibu.


 Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Abdullahi Kiyawa Haruna, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Laraba, 3 ga watan Janairu, 2024, ya ce Haruna, na karamar hukumar Dala ta jihar, ya daba wa malamin wuka har lahira bayan marigayin ya yi kokarin hana shi da ’yan kungiyarsa shan tabar wiwi a kusa da harabar Masallacin.


 “A ranar 31/12/2023 da misalin karfe 1930 ne aka samu rahoto daga wani Musa Yunusa ‘m’ na Jakara Quarters Kano cewa a ranar da misalin karfe 1900, Yusuf Haruna ya kai hari tare da daba wa wani Malam Sani Mohammed Shuaibu mai shekaru 45 wuka mai kaifi a bayansa yayin da yake alwala, kawai saboda wanda abin ya shafa ya gargade shi da 'yan kungiyarsa da su daina shan tabar wiwi a kusa da harabar Masallacin," in ji sanarwar.


 “Saboda haka, wanda abin ya shafa ya samu rauni sosai, aka garzaya da shi asibitin kwararru na Murtala Muhammed, kuma likita ya tabbatar da mutuwarsa.


 “Lamarin ya girgiza al’umma, kuma jami’an mu sun yi bakin kokarinsu wajen zakulo maharin tare da kama shi.  Wannan kamun ya shaida mana jajircewarmu na kare martabar rayuwa da kuma tabbatar da adalci ga wadanda irin wadannan munanan ayyuka suka shafa.”


PPRO ya kara da cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Mohammed Usaini Gumel, ya baiwa jama’a tabbacin hukumar ta dau alwashin gudanar da cikakken bincike kan lamarin.


 "Bugu da ƙari, za mu yi aiki tuƙuru don tattara kwararan hujjoji don tabbatar da nasarar gurfanar da mutanen da aka kama."


 "Manufarmu ba wai kawai mu gurfanar da wadanda suka aikata laifin a gaban kuliya ba ne, har ma da zama kange ga wasu da za su yi tunanin irin wannan aika-aikar."

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN