Shugaban K. Hukumar Birnin kebbi Alh Aminu Ahmed S. Fada ya kai ziyarar Ta'aziyya gidan mutumin da aka kashe a Badariya


Shugaban karamar hukumar mulki ta Birnin kebbi Alhaji Aminu Ahmed S. Fada tare da DPM da Director Agric na karamar hukumar sun kai ziyarar jaje ga iyalin Malam Abubakar (Buba) wanda aka kashe a Badariya.

Alhaji Aminu ya gana da Yan uwan mamacin inda ya roki Allah ya gafarta masa kuma ya ba iyalinsa ikon jure wannan rashi.

Cikin wadanda suka tarbi shugaban karamar hukumar Birnin kebbi a wajen ta'aziyyar har da shugaban kungiyar Miyetti Allah reshen karamar hukumar Birnin kebbi.

Shafin labarai na isyaku.com ya ruwaito cewa cewa wani mutum mai suna Usman Muhammed ne ya farmaki Abubakar (Buba) a gidansa inda ya kashe shi bayan ya caka masa wuka a wurare da dama a jikinsa a gaban Mahaifiyarsa da matarsa. 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN