Da an hana Abba Gida-Gida mulkin Kano, da Najeriya ta kama da wuta, inji Buba Galadima

Photo Credit: Channels TV

Fitaccen jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya bayyana ra’ayinsa da hangensa kan illar da ka iya biyo bayan hukuncin da kotun koli ta yanke a baya-bayan nan, musamman game da rikicin ‘yan takarar gwamna a jihar Kano. Legit Hausa ya wallafa.

A nasa ra'ayin, kasar na iya fuskantar tashin hankali idan har kotun koli ta yanke hukuncin tsige gwamna Abba Yusuf na jihar Kano a gagarumin hukuncin da ta yanke a ranar Juma'ar da ta gabata.

Galadima ya mika sakon taya murna ga shugaban kasa Bola Tinubu na jam’iyyar APC bisa mutunta ‘yancin kan tsagin shari’a, musamman yadda lamarin ya shafi Nasir Gawuna, dan jam’iyyar APC

Da yake magana a Channels TV ya ce:

“Ina taya mai girma shugaban kasa na rashin yin katsalandan a bangaren shari’a domin Najeriya za ta iya kamawa da wuta a yanzu idan abin da ya faru ranar Juma’a bai faru ba.
"Ina taya shi (Tinubu) murna saboda yana da karfin hali kuma za ka ga cewa zaman lafiya ya mamaye duk fadin Najeriya kuma darajarmu ta 

Daga cikin kararraki takwas, na Kano, Zamfara da Filato sun ba da mamaki yayin da kotun koli ta yi fatali da hukuncin da kotun kararrakin zabe da kotun daukaka kara suka yanke na mayar da gwamnonin jihohin uku.

Kafin yanke hukuncin ranar Juma'a kan rikicin gwamnan Kano, tuni tashin hankali ya yi kamari a Kano, inda mabiya NNPP ke nuna damuwarsu.

Da yake magana a shirin Sunday Politcs na Channels TV, Galadima ya ce akwai wani shiri na kwace mulki daga hannun jam’iyyar NNPP a Kano kasancewar jam’iyyar ta kori APC daga kan karagar mulki a zaben da ya gabata.Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN