Badakalar Kwangila: Mutane sun dage dole a fatattaki Minista na 2 a Gwamnatin APC


Wasu mutane sun huro wuta dole sai shugaban kasa ya fatattaki Hon. Olubunmi Tunji-Ojo daga matsayin ministan cikin gida.

Masu wannan kira a kafafen sadarwa na yanar gizo sun ce ya kamata a kori ministan saboda kwangilar da aka ba tsohon kamfaninsa. Legit Hausa ya wallafa.

Tonye Barcanista ya bada misali da Barth Nnaji wanda ya rasa kujerarsa a lokacin yana Ministan makamashi a mulkin Goodluck Jonathan.

Gwamnatin Dr. Jonathan ta saida kamfanin wuta ga ‘yan kasuwa, a 2012 aka gano Nnaji ya taba samun alaka da kamfanin Geometric Power.

Duk da ya bar kamfanin lantarkin, a kan haka aka tilastawa ministan yin murabus, kuma NCP ta soke cinikin saboda jin tsoron ayi son kai.

Da yake magana a dandalin X, ‘dan adawan ya bukaci Olubunmi Tunji-Ojo ya yi murabus bayan an gayyace shi zuwa fadar Aso Villa.

Bulama Bukarti wanda masanin shari’a ne a Birtaniya, ya yi irin wannan kira a shafin X, ya ce akwai bukatar dakatar da ministan cikin gidan.

Dalibin shari’ar a jami’ar SOAS yana so shugaban kasa yana so a binciki kwangilolin da aka bada sa’ilin da Betta Edu ta ke kujerar minista.

Ra’ayin lauyan shi ne doka ba amince jami’in gwamnati ya cusa kan shi a inda za a iya samun cin karo tsakanin aikin ofis da ra’ayin kansa ba.

Wannan shi ne ra’ayin Yinka Chukwuemeka Ogunnubi, ya ce ko da ministan ya bar kamfanin, ba zai rasa ta-cewa wajen samun kwangila ba.

Da mu ka yi magana da Dr. Mohammed Alhaji, ya ce akwai bukatar a samar da dakunan shan magani a kowace mazaba a Najeriya.

Idan ana so ayi hakan, masanin kiwon lafiyan ya kawo shawarar a soke ma’aikatar jin-kai, a karkatar da kudin zuwa hukumar NPHCDA.

Likitan ya ce wannan zai fi bada damar a binciki idan kudin su ke shiga kuma a iya magance matsalolin kiwon lafiya da ake fama da su.

Olubunmi Tunji-Ojo ne ya kafa kamfanin New Planet Projects Ltd wanda ya samu kwangilar N438m daga ministar jin kai ta kasa.

Ministan harkokin gidan ya ce ya yi murabus daga kamfanin, sai dai ya bar baya da kura da ya ce mai dakinsa ce darektar kamfanin.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN