Lamarin ya faru ne a unguwar Idi Orogbo da ke Araromi a cikin Sango-Ota a ranar Talata, 30 ga Janairu, 2024.
Wasu majiyoyi na kusa da marigayin sun shaida wa jaridar Nigerian Tribune cewa an gano gawar D1 a rataye a jikin wani gado a daya daga cikin shagunan sa guda biyu da ya kwana.
Majiyar ta ce matakin da D1 ya yanke na kawo karshen rayuwarsa watakila ba zai rasa nasaba da bashin da ya ci ba.
An kuma tattaro cewa marigayin na shirin rasa gidansa ne sakamakon bashin da ake binsa.
"Matar sa ce ta gano D1 a rataye a saman rufin, wacce ta zo duba shi," in ji majiyar.
“Tun wani lokaci yanzu yana fama da matsalar kudi sosai, yana da shaguna guda biyu inda yake siyar da CD na bidiyo.
Wani Mazauni garin ya ce an kai rahoton lamarin a ofishin ‘yan sanda reshen Sango Ota.
From ISYAKU.COM