Naira ta kara faduwa a ranar Litinin, 29 ga watan Janairu, yayin da aka canza ta a kan N1506/$ daga N1,410 da aka sayar da ita a ranar da ta gabata a kasuwannin bayan fage.
A kasuwannin hada-hadar kudi, an yi musanyar Naira a kan N1,349 daga N891.90/$ da aka yi cinikinta a ranar da ta gabata. Lamari da ya haifar da babban gibin qdarajar N1,410.
Hakan dai na faruwa ne a daidai lokacin da babban bankin Najeriya (CBN) ya saki dala miliyan 500 ga sassa daban-daban domin magance koma bayan da aka tabbatar a hada-hadar kudaden waje (forex).
From ISYAKU.COM