Zan cire duk wani jami’in da ya sayar da motar gwamnati – Gwamnan Kebbi ya yi gargadin


Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris  ya ce zai cire duk wani kwamishina da ya sayar da motar hukuma da aka ba shi.  Ya kuma raba babura 700 ga ‘yan kungiyar ’yan banga a jihar.


 Wannan na kunshe ne a cikin rahoton Daily Trust cewa Gwamna Nasiru Idris na jihar Kebbi a ranar Laraba ya ce ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen korar duk wani kwamishinan da ya siyar da motocin hukuma da gwamnatin jihar ta ba shi.


 Ya kuma sha alwashin korar duk wanda ya ki ziyartar mazabar sa domin jin ta bakin jama'arsa  kan manufofi da shirye-shiryen gwamnati.


 Gwamnan ya yi wannan gargadin ne a jiya a Birnin Kebbi yayin da yake gabatar da motoci guda 26 da gwamnatin jihar ta saya wa kwamishinonin.


 Ya ce, “Motocin hukuma da muka ba ku sune don ku ziyarci mutanen ku akai-akai kuma ku dawo mana da bukatunsu.


 "Ba zan yi jinkirin cire duk wani kwamishinan da ya sayar da motar da muka ba ku ba".


 Gwamnan ya kuma raba babura 700 ga kungiyar yan banga domin su samu damar gudanar da ayyukansu na tsaro.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN