An kama dan shekara 25 yana lalata da saniya turmi-tabarya, garin gudu ya fadi shanaye suka tattake shi


An kama wani mutum yana lalata da saniya kuma a yanzu an hana shi mallakar dabbobi tsawon shekaru 10.


 An gano Liam Brown a cikin wani yanayi maras kyau, tare da zazzalo wandonsa "yana yin jima'i da saniya a fili," wata kotu ta saurari karar a wannan makon.


 Sai dai matashin mai shekaru 25, bai samu kyakkyawan karshe ba yayin da ya yi kokarin tserewa daga hannun mai gonar da ya fusata ta hanyar tsallakewa zuwa wani bangare na gonar, sai dai wasu shanun suka tattake shi.


 Daga nan aka same shi kwance a kasa yana kururuwa: 


 Daga baya an tuhumi Brown da yin jima'i da dabba mai rai da kuma haifar da wahala da ba dole ba ga dabbar saboda abin da ya faru a gona a Burton, Dorset.


 Haƙiƙa an kama Brown a kamaran CCTV, wanda aka kafa yayin da masu gonaki ke zargin ana lalata da shanunsu. Kuma an tabbatar da zargin a farkon sa’o’in 12 ga Yuni, 2022.


 An dauki samfurin DNA kuma an tabbatar da cewa Brown ya yi lalata, "saduwa" da dabbar.

 A taƙaice, alkali Keith Cutler ya ce: “Wannan lamari ne mai ban tsoro, ban mamaki da damuwa.  Mutumin da ke cikin shekarun ka yana shiga cikin wannan hali - Na tabbata za ka waiwaya baya da kunya.


Daga karshe Kotu ta haramta masa mallakar dabbobi har tsawon shekara 10. An ba shi umarnin yi wa al'umma hidima na tsawon watanni 36 kuma an ce ya yi aikin sa'o'i 15 na rashin biya.  An kuma umarce shi da ya biya fam 600 a matsayin diyya.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN