Za a fara dandake masu yin fyade a Kaduna

 

Gwamnatin jihar Kaduna ta jaddada shirinta na gudanar da aikin tiyatar cire marena ga mazajen da suka yi fyade da kuma tiyatar salpingectomy ga takwarorinsu mata.

 Ku tuna cewa a shekarar 2022, tsohon Gwamnan jihar, Nasir El-Rufai ya sanya hannu kan dokar da aka yi wa gyaran fuska ta 2020 wacce ta tanadi yin tiyatar cire marena ga maza da cire bututun fallopian ga mata masu yiwa yara fyade bayan an same su da laifi.

 A watan Nuwamba 2020, majalisar dokokin Kaduna ta amince da yanke hukunci a matsayin hukunci ga duk wanda aka samu da laifin fyade a jihar.

 Kwamishiniyar aiyuka da ci gaban jama’a, Madam Rabi Salisu, ta bayyana hakan a wani taron masu ruwa da tsaki na jinsi da aka gudanar a Kaduna a ranar Alhamis 30 ga watan Nuwamba, 2023.

 Ma’aikatarta ce ta shirya taron kolin, tare da hadin gwiwar Cibiyar Hadin Kai da Shirye-shiryen Lafiya (CIHP).

 Salisu ta ce matakin na ladabtarwa na kunshe ne a cikin dokar hana cin zarafin jama’a da gwamnatin jihar Kaduna ta kafa (VAPPL), ta shekarar 2018.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN