An daure Sarkin Fulani da yan uwansa 2 rai da rai kan garkuwa da mutane


Wata babbar kotu da ke zamanta a Ilorin ta yanke hukuncin daurin rai-da-rai ga Sarkin Fulanin Kwara, Usman Adamu, da dan uwansa, da wani Gidaddo Idris, bisa samun su da laifin hada baki da kuma garkuwa da mutane.

 An gurfanar da su ne kuma aka yanke musu hukuncin yin garkuwa da Abubakar Ahmad wani lokaci a shekarar 2022.

 An ce wadanda aka yanke wa hukuncin sun karbi kudin fansa nera miliyan daya kafin su sako wanda aka kama, wanda ya shafe kwanaki 20 a hannunsu.

 Daraktan shigar da kara na jihar Kwara (DPP), Idowu Ayoola, ya gabatar da wadanda ake kara a gaban kotu bisa zargin hada baki wajen yin garkuwa da mutane.

 A hukuncin da ya yanke, Mai shari’a Adenike Akinpelu, ya ce shaidun da masu gabatar da kara suka gabatar sun tabbatar da cewa dukkan wadanda ake tuhuma uku sun hada baki ne don aikata laifin.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN