Yanzun nan: Hisbah ta kama dan Acaba da ya zarce da yar shekara 12 cikin daji yayi mata fyade a Birnin kebbi


Jami’an hukumar Hisbah ta jihar Kebbi sun kama wani mutum mai suna Muhammad Dahiru, mai shekaru 33 bisa zargin yiwa wata yarinya ‘yar shekara 12 fyade a Birnin-kebbi.

Hisbah ta bayyana a shafinta na Facebook cewa wanda aka kama ya dauki yarinyar a Kabu-kabu daga nan sai ya zarce da ita zuwa cikin daji inda ya yi mata fyade.

 An kama Dahiru dan karamar hukumar Koko/Besse a jihar a ranar Litinin, 11 ga Disamba, 2023.

 Dahiru ya amsa laifinsa kuma an mika shi ga ‘yan sanda domin ci gaba da bincike da gurfanar da shi gaban kuliya.

Nafiu Zaki, shugaban kungiyar yan Acaba na jihar Kebbi ya ce basu da masaaniya game da lamarin balle su iya tabbatar da sahihancin wanda aka kama ko ainihin dan kungiyar yan Acaba na jihar Kebbi ne ko.akasin haka kawo lokacin rubuta wannan rahotu.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN