Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta damke wasu mashahuran barayin POS da wayar salula su hudu a karamar hukumar Kazaure da ke jihar.
Kakakin rundunar Yan sandan jihar, ASP Abubakar Isah, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Asabar, 16 ga watan Disamba, 2023, ya ce wadanda ake zargin sun amsa cewa sun shafe shekaru hudu suna aikin.
A cewar PPRO, wadanda ake zargin wadanda kuma suka kware wajen fasa gidaje da sata, sun addabi al’ummar Kanti, Katoge, da Shagari Quarters duk a cikin babban birnin Kazaure.
Ya ce wadanda aka kama sun hada da
“Najib Murtala ‘m’ dan shekara 23 a Galandi Quarters tare da wasu guda uku (3), kuma an same su da na’urar P.O.S, da wayoyin hannu guda biyu (2) na android".
“Bincike ya nuna cewa wadanda ake zargin sun kware wajen fasa gidaje da sata kuma sun addabi al’ummar Kanti, Katoge, da Shagari Quarters duk a cikin babban birnin Kazaure".
"Dukkan wadanda ake zargin za a gurfanar da su a gaban kotu bayan gudanar da bincike na gaskiya a sashin binciken manyan laifuka na jiha (SCID) Dutse”.
From ISYAKU.COM