Yan Najeriya na fama da matsin tattalin arziki yayin da gwamnatin Tinubu ke sharholiya - Rahoto


Halin da tattalin arzikin Najeriya yake ciki ya tilasta 'yan kasar daukar matakan rayuwa a ciki, da yawa daga tsare-tsaren gwamnatin kasar na samun suka daga jama'a. Legit Hausa ya wallafa.

Jaridar Vanguard ta fara nazarin mukarraban gwamnati da Shugaba Tinubu ya nada, da kuma shirinsa na yin garambawul a hukumomi, ma'aikatu da bangarori na gwamnati.

Tun daga shekarar 1999 ba a taba samun gwamnati mai tarin mukarrabai irin ta Tinubu ba, ko ministoci akwai 48 yanzu a kasar, kamar yadda Majalisar Tarayya ta tantance su.

Otel din UNGA: A watan satumba, gwamnati ta kashe naira miliyan 390.7 kan dakunan kwanan wakilan data tura taron majalisar dinkin duniya (UNGA) a birnin New York, rahoton Vanguard.

Sakataren fadar shugaban kasa, Adebiyi O. Olufunso ya sanar da hakan a ranar 11 ga watan Satumba, inda masu fashin baki ke ganin kudaden sun yi yawa, musamman a halin matsin tattali da kasar ke fama da shi.

Taron COP28 a Dubai: Najeriya ta kashe makudan kudade wajen tura wakilai karon dumamar yanayi a Dubai. Duk da an rawaito wakilai 1,411 ta tuwa, gwamnatin kasar ta ce mutum 422 kawai ta dauki nauyin su.

Jirgin ruwan alfarma na shugaban kasa: A watan Nuwamba, aka ware naira biliyan 5.1 don siya wa shugaban kasa jirgin ruwa na alfarma.

Duk da cewa rahoto ya nuna tun a zamanin mai girma Buhari aka amince a sayi jirgin, sai dai majalisar tarayya ta dau aniyar karkatar da kudin zuwa asusun tallafa wa daliba.

An ware wa kowanne dan majalisar tarayya naira miliyan 160 don sayen manyan motocin alfarma, ban da makudan kudi na alawus da ake ba su.

Sai kuma a hannu daya, gidan zaman mataimakin shugaban kasa a Abuja ya lakume naira biliyan 20.5 wajen gyara, haka aka ware naira biliyan 3 don gyara gidan shi na Legas.

Kasafin 2024: A kasafin kudin 2024 kuwa, 'yan Najeriya sun yi korafi kan yadda aka ware naira biliyan 319.28 don watsa labarai, walwala da kiwon lafiya a fadar shugaban kasa da wasu bangarori na gwamnati.

An kuma ware naira biliyan 61.29 don gyare-gyare da gine-gine; sai kuma tafiye-tafiyen shugaba Tinubu da mataimakinsa zuwa kasar waje zai lakume naira biliyan 7.5.

Fannin abinci a ma'aikatun Gwamnatin Tarayya kuwa ya samu naira biliyan 5.84 yayin da fadar shugaban kasa ta samu naira biliyan 6.2 don hawan motoci.

Sai dai Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da muhimmancin kasafin 2024 na kawo babban ci gaba a tattalin arziki da gina Najeriya, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN