‘Yan bindiga sun kona wata mata da ‘ya’yanta guda biyu da kuma surukanta har lahira a Sokoto


Wasu ‘yan bindiga sun kashe akalla mutane 12 da suka hada da mace daya da ‘ya’yanta biyu da kuma sirikanta a kauyen Kurya da ke karamar hukumar Rabbah ta jihar Sakkwato.


 Wani mazaunin unguwar, Yusuf Kurya, ya ce ‘yan bindigar sun kai hari kauyen ne a daren Lahadi, 24 ga watan Disamba, 2023.


 “Lamarin ya faru ne a daren Lahadi da misalin karfe 8:30 na dare lokacin da ‘yan bindigar suka kai hari kauyen mu da yawa, suna harbi lokaci-lokaci,” kamar yadda ya shaida wa jaridar Punch ranar Talata.


 “Sun kashe kusan mutane 12 a yayin da aka kona hudu daga cikinsu da ransu.


 “Sun kuma yi awon gaba da wasu mata uku a kauyen yayin da kuma aka yi awon gaba da dabbobi da ba a tantance adadinsu ba.”


 Ya ce biyo bayan kiran da mazauna yankin suka yi, an tattara dakarun Operation Hadarin Daji inda suka bi su, inda suka kashe wasu daga cikin ‘yan bindigar.


 Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto, ASP Ahmed Rufa’i, wanda ya tabbatar da faruwar harin, ya ce daga bayanan karshe da ya samu daga kauyen, tuni aka tabbatar da mutuwar mutane bakwai tare da yuwuwar alkaluman su karu.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN