Dan Majalisa Barista Maisudan zai dauki nauyin wasu matasa zuwa karatun gaba da Sakandare har da wasu ayyukan alhairi


Danmajalisar dokoki mai wakiltar Mazabar Suru, Hon Barr Faruku Abubakar Maisudan, Shugaban kwamitocin Shari’a da Raya Karkara zai dauki nauyin karatun matasa maza da mata daga lungu da sako na karamar hukumar mulki ta Suru zuwa makarantun gaba da Secondary domin karo karatu a fannin likitanci, engineering, karantarwa da sauran fannonin ilimi. 

Maisudan zai Dauki nauyin dalibai 20 zuwa College of Health Sciences and Technology Jega, dalibai 20 zuwa JIBWIS College of Education Jega, dalibai 20 zuwa Adamu Augie College of Education Argungu da kuma dalibai 20 zuwa Kebbi State Polytechnic Dakingari.

Da yake gabatar da jawabi yayin kaddamar da Selection Committee a garin Dakingari, Hon Maisudan yace ya yanke wannan hukunci ne  domin cika alkawalin da yayi a lokacin da yake yakin neman azabeshi dukuma kokarinsa naganin ya bada tasa gudummuwa a fannin Ilimi.

Hakazalika Maisudan yayi alwashin rabawa masu son zuwa Jami’a JAMB Form idan lokaci yayi kyauta.

A bangare daya, Hon Maisudan ya dauki nauyi yiwa mutum 500 register kiwon lafiya da hukumar Kebbi State Contributory Healthcare Management Agency (KECHEMA) amatsayin wani bangare na gudummuwarsa a bangaren kiwon lafiya.

Hon Maisudan yakara dacewa a wani bangare na marawa Gwamna Comrade Nasir Kauran Gwandu na muradun sa na ciyarda jihar nan gaba ya yanke shawarar ganin cewa kowace mazaba ta samu akalla mata biyu wayanda suka samu korewar kiwon lafiya da zasu duba mata masu juna biyu tare da samar musu da magani kyauta.

Hon Maisudan yayi kira ga matasa masu shawar shiga jami'a, da su kasance cikin shiri domin kowane lokaci aka fara sayarda form din za’a samar dasu kyauta.

Dayake gabatarda jawabinsa jim kadan bayan gabatar masa da wasu daga cikin forms din Shugaban Jam'iyar APC na Suru Local Government Alh Bako Bala ya jinjinawa dan Majalisar akan hangen nesan sa na bullowa da wannan matakin na daukar nauyin matasa domin samun karatu matakin gaba da Secondary.

Alh Bako Bala ya baiyana cewa lallai karamar hukumar mulki ta Suru basuyi zaben tumun dare ba saboda tun yanzu kwalliyarsu tafara biyan kudin sabulu. Haka zalika ya yaba da Danmajalisar akan mutunta jam'iyya ako yaushe.

Ahmad Usman Mairukubta
Special Assistant to the Executive Governor and Media Advisor to Hon Member Suru LG Constituency.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN