Yadda tsohon sufeton yan sanda ya zama mabaraci saboda tsananin matsin tattalin arziki


 Sauyin rayuwa ya sa wani Sunday Ogwo Okpalle, sufetan 'yan sanda mai anini biyu da ya koma wa mabaraci a kan titunan jihar Niger..

Sunday Okpalle, ya shafe kusan rasuwarsa yana aikin dan sanda, matsayin mai bayar da hannu a kan titi a jihar. Legit Hausa ya wallafa.

A safiyar ranar Talata, wakilin jaridar Punch ya ci karo da Okpalle, wanda ke bin masu motoci, Keke Napep da 'yan acaba yana rokon kudin da zai ci abinci

Ku taimake ni ko na sami na cin abinci," ya ke nanata wa masu ababen hawan, wadanda ba sa ko kula shi.

Yayin da wasu suka ba shi taimako daga abin da suke da shi, wasu kuma sukan ce:

"Ku kyale shi, haka yake bara a nan kullum, ba ya ko gajiya."

Da ya zanta da wakilin Punch, ya shaida masa cewa tsananin rayuwar da ya shiga ne ya tilasta shi yin bara, rashin yin hakan na iya saka shi kwana da yunwa.

Batu kan fansho da ya ke karba kuwa, ya tabbatar da cewa ana tura masa naira dubu talatin ne kuma kudin na zuwa ne a kurarren lokaci.

"Rayuwa ba ta yi mun kyau ba, shekara biyar da yin ritaya yanzu, ina da yara biyar da mata daya, amma sai na yi bara muke cin abinci.

"A lokacin da nake aiki, nakan samu naira dubu uku zuwa hudu kafin na tashi aikin ranar, amma yanzu ko sisi bana samu."

A cewar Mr Okpalle, kamar yadda Legit ta ruwaito, inda ya kara da cewa:

"Sai da na yi shekara daya da rabi sannan na samu naira miliyan 1.7 na giratuti madadin miliyan 6. Haka na hakura, daga nan duk wata ake tura mun naira dubu talatin kudin fansho.

"Kudi sun zo sun kare saboda dawaniyar karatun yara da hidimar gida, karshe dai dole na dawo yin bara don ciyar da iyalina."

A karshe ya roki gwamnatin tarayya da ta taimaka ta biya sa karashen kudin giratutinsa ko ya samu ya farfado daga wannan bakin talaucin da ya ke ciki.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN