Yanzu: An nemi ministan tsaron Tinubu ya yi murabus kan kisan masu Maulidi a Kaduna

 

Masu zanga-zanga sun mamaye zauren majalisar dokokin tarayya da ke Abuja a ranar Laraba, 6 ga watan Disamba, kan kisan bayin Allah da dama da jirgin sojoji ya yi a ranar Lahadi. Legit Hausa ya wallafa.

Masu zanga-zangar sun bukaci a yi wa wadanda aka kashe adalci sannan sun nemi ministan tsaro, Abubakar Badaru, da ya tashi ya yi abun da ya rataya a wuyansa ko ya yi murabus, rahoton Daily Trust.

A halin da ake ciki, fiye da mutum 90 ne aka kashe a kauyen Tudun Biri a yankin Rigasa da ke karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna bayan jirgin soji ya jefa bam kan masu bikin maulidi a daren ranar Lahadi.

Mazauna yankin sun ce mutum fiye da 60 ne suka jikkata a harin. Tuni rundunar soji ta dauki alhakin jefa bam din, amma ta ki yin karin bayani.

Da yake jawabi ga manema labarai, jagoran masu zanga-zangar karkashin inuwar kungiyar matasan Najeriya (NYCN) yankin arewa maso yamma, da kungiyar matasan arewa, Nasir Ishaku, ya nemi ayi wa wadanda abun ya ritsa da su adalci, rahoton Punch.

Ya ce kisan bayin Allah yan Najeriya, musamman a yankin arewacin kasar da ake yawan yi a kullun ba abun yarda bane sannan cewa ba za a sake lamuntan hakan ba.

Ishaku ya bukaci Majalisar dokokin tarayya da ta yi bincike kan kisan ranar Lahadi da aka yi a Kaduna sannan ta dauki kwararan mataki domin ceto kasar.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN