Ta sake faruwa: Yan bindiga sun yi awon gaba da mawaki da ƴan amshinsa cikin ayarin motocinsu a jihar arewa


An shiga firgici a safiyar Litinin kan rahotannin da ke cewa an yi garkuwa da wani mawakin Juju dan Najeriya, Omoba De Jombo Beats tare da masu masa kida a ranar Lahadi.

Rahotannin da ke yawo a yanar gizo na cewa, mawakin da ‘yan tawagarsa na dawowa daga wani taro lokacin da aka yi garkuwa da su. Legit Hausa ya wallafa.

Wani mawaki da aka fi sani da Boyebest, ya wallafa labarin a shafinsa na Instagram inda ya koka kan wannan lamari da ya faru a karshen makon da ya gabata.

Boye Best ya yi wa labarin nasa taken, “An yi garkuwa da mawaki da dukkan tawagar makadansa. Lallai Najeriya ta lalace."

An gano cewa wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba ne suka yi garkuwa da su bayan sun yi wani wasa a Abuja a karshen mako, cewar Vanguard.

Boye Best ya ce:

"An yi garkuwa da Omoba De Jombo Beats da makadansa a hanyarsu ta zuwa Kogi daga Abuja bayan yin wasa a ranar Lahadi.
"Muna neman taimakon ku jama'a saboda masu garkuwan na neman naira miliyan 10 kudin fansa kan kowanne mutum daya."

A karshe Boye Best ya yi wa mawakin da masu masa kida addu'ar fita daga hannun masu garkuwa da mutanen lami lafiya.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN