Ta faru: Ministan Tinubu ya yi murabus daga mukaminsa, bayanai sun fito


Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Simon Lalong, ya yi murabus a hukumance, wanda ke nuni da ficewa daga mamba a majalisar ministocin shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu.

Lalong, tsohon gwamnan jihar Filato, ya zabi zama dan majalisar dattawan Filato ta Kudu bayan hukuncin kotu da ta ba shi nasara a zaben da ya gabata. Legit Hausa ya wallafa.

Ana sa ran shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio zai rantsar da Lalong a cikin wannan mako.

Duk da cewa tun farko INEC ta ayyana shi a matsayin wanda ya sha kaye a zaben da aka gudanar a watan Fabrairu, Lalong ya shigar da kara kan sakamakon zaben inda a karshe ya samu nasara a Kotun Daukaka Kara.

Lalong ya mika takardar murabus dinsa ne a ranar Larabar da ta gabata a daidai lokacin da yake shirin karbar sabon mukaminsa a majalisar dokokin kasar.

An tabbatar da murabus din Lalong ta hanyar wani sako a shafin X, wanda wani mai taimaka wa shugaban kasa Imran Muhammad, ya rubuta kamar haka:

“Shugaba Tinubu ya amince da murabus din ministan kwadago da samar da ayyuka, Simon Lalong daga majalisar ministoci."

A watan da ya gabata ne dai Gwamna Lalong ya samu takardar shedar nasarar cin zabe sakamakon umarnin da Kotun Daukaka Kara ta baiwa hukumar zaben.

Hakan ya biyo bayan soke zaben Air Vice Marshall Napoleon Bali daga jam'iyyar PDP, lamarin da ya sa Lalong ya dare kan kujerar sanatan.

A ziyarar da ya kai hedikwatar INEC, Lalong ya samu rakiyar iyalansa da suka hada da matarsa ​​Regina da ‘ya’yansa, da wasu jigogin jam'iyyar APC.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN