Ministoci 10 da za su tashi da 86% na duka kudin da za a kashe a Najeriya a 2024


Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da kundin kasafin kudin da ke dauke da bayanan abin da ake so a kashe a Najeriya a shekarar 2024.

Da The Cable ta yi nazarin kasafin kudin na 2024 da kyau, an fahimci cewa wasu manya ma’aikatu 10 za su tashi da kaso mafi tsoka a ciki.

An warewa wadannan ma’aikatun tarayya N20.7tr daga cikin kasafin kudin na N24.07, hakan yana nufin su kadai za su samu har 86.3% . Legit Hausa ya wallafa.

Ga jerin ma’aikatun da su ka fi samun kudi:

1. Ma’aikatar kudi

Ma’aikatar kudi da tattalin arziki ta samu N9.33tr a kasafin 2024. Mafi yawan kudin za su tafi ne a biyan albashi, N808.92bn aka ware domin ayyuka.

2. Ma’aikatar kasafi

N4.45 aka warewa ma’aikatar da ke shirya kasafin da sauran tsare-tsaren tattalin arziki. Ma’aikata za su ci N1.79tr, sannan za ayi ayyuka na N1.88tr.

3. Ma’aikatar tsaro

Idan an samu yadda ake so a majalisar tarayya, gwamnatin Bola Ahmed Tinubu za ta kashewa ma’aikatar harkar tsaro N1.58tr a shekara mai zuwa.

4. Ma’aikatar ilmi

Binciken ya nuna N1.44tr aka ware domin sha’anin ilmi ya bunkasa a kasar, amma N1.04tr zai tafi wajen albashi ne, watakila shiyasa ASUU ta ke korafi.

5. Ma’aikatar lafiya
 da walwalar jama’a

Jaridar ta ce Farfesa Muhammad Ali Pate ya samu N1.23tr a kasafin kudin da aka tsata. Gwamnatin tarayya ta yi alkawarin kason zai karu nan gaba.

6. Ma’aikatar harkokin ‘yan sanda

Abin da za a kashewa ma’aikatar ‘yan sanda a 2024 zai iya kai N938.74bn wanda mafi yawa za su tafi ne wajen biyan albashin jami’an tsaron kasar.

7. Ma’aikatar ayyuka

Daga cikin N657.23bn da aka warewa Dave Umahi, ana sa rai ma’aikatar ayyuka za ta kashe N612.85bn domin yin kwangilolin tituna da gadoji a jihohi.

8. Ma’aikatar cikin gida

A kasafin kudin shekara mai zuwa, N461.99bn za su tafi ga ma’aikatar harkokin cikin gida. Legit ta fahimci hakkokin ma’aikata ne za su cinye kusan 80%.

9. Ma’aikatar aikin gona

Domin ganin an samar da isasshen abinci daga gonaki, Sanata Abubakar Kyari zai so ma’aikatarsa ta kashe akalla N362.94bn a shekarar da za a shiga.

10. Ma’aikatar Neja Delta

Ma’aikatar da ta rufe goman farko ita ce ta harkokin Neja-Delta da za a kashewa N346.12bn. Abin mamaki, N18bn kadai aka yi tanadi domin ayyuka.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN