Yanzun nan: Gobara ta babbake ofisoshi a sakateriyar ƙaramar hukuma a jihar Kano


Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da cewa wutar da ta kama da safiyar ranar Laraba ta ƙone ofisoshi 17 a sakateriyar karamar hukumar Gwale. Legit Hausa ya wallafa.

Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar kwana-kwana, Alhaji Saminu Abdullahi, shi ne ya tabbatar da aukuwar lamarin ga hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) a Kano.

Abdullahi ya bayyana cewa gobarar ta tashi a sakatariyar ƙaramar hukumar a awannin farko na safiyar ranar Laraba, 13 ga watan Disamba, 2023.

Punch ta tattaro Abdullahi na cewa:

"Mun samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 3:43 na safiya daga wani mai suna Abdullahi Hassan, wanda ya shaida mana cewa wuta ta kama a sakateriyar Gwale."

"Nan take bayan samun wannan bayanan muka tura motar kashe wuta zuwa wurin da misalin ƙarfe 3:46 na safe domin shawo kan lamarin cikin hanzari."

Abdullahi ya ce wurin da aka yi amfani da shi a matsayin ofis mai tsawon ƙafa 300 x 200 da sauransu, wanda a jimulla ya kai ofisoshi 17, ya ƙone gaba ɗaya.

Haka nan kuma ya bayyana cewa wasu motoci uku da aka ajiye a sakatareyar wutar ta shafe su amma ba sosai ba.

Mai magana da yawun hukumar kashe gobarar ya ambaci sunayen motocin da wutar ta taɓa, wanda suka haɗa da 406 Peugeot guda ɗaya, Bas guda ɗaya da motar ujila.

Ya ce a halin yanzu hukumar ta fara bincike domin gano musabbabin abin da ya kawo tashin gobara a sakateriyar Gwale, cewar rahoton Daily Post.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN