Masu garkuwa sun lakada wa Basarake duka har ya suma sakamakon rashin cika kudin fansa bayan sace shi da iyalinsa

 

Masu garkuwa da mutanen da suka sace Sarkin Fili da ke unguwar Mpape a karamar hukumar Bwari a babban birnin tarayya Abuja sun lakada wa basaraken duka har ya suma kan rashin cikar kudin fansa da iyalansa suka biya.

 Ku tuna cewa an sace Basaraken, Peter David tare da matarsa, 'ya'yansu uku, da kuma wasu mazauna garin hudu, yayin da aka kashe mutane biyu.

 Da take zantawa da Daily trust a ranar Talata, 5 ga watan Disamba,  Matar Sarkin, Aisha Peter, wadda aka sake ta bayan kwanaki biyu domin ta neman kudin fansa N100m, ta ce masu garkuwa da mutane sun yi wa mijin nata dukan tsiya saboda rashin samun kudin da ta yi.  kudin da ta tara N8m ne kawai.

 “Na kira su ta waya da safiyar yau domin sanar da su cewa N8m ne kawai na samu, kuma da na bukaci na yi magana da shi, ‘yarmu ‘yar shekara 14 ce ta iya magana, sai ta ce min mijina ya kasa magana sakamakon duka,” ta bayyana.

 An kuma kara da cewa, babu daya daga cikin mazauna garin hudu da aka yi garkuwa da su da masu garkuwan suka kubutar da su, wadanda suka sanya wa kowannen su kudin fansa N50m.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN